Tuesday, June 23, 2009

SAUTIN HAUSA
YAKA IYA YIN RUBUTU MAI MAANA,KO TALLA AKAN WANNAN SHAFIN WANDA YA KUNSHI WASANHAUSA, ADABI, RAYUWAR MATA, KO YANAYIN SIYASAR BAHAUSHE- Ne me mu akan wanann email din sautinhausa@gmail.com, nauku1991@yaho
Daga salisu Abubakar Nauku


MALAM KABIRU NAKWANGO
Daya daga cikin uwaye a harkar wasan hausa


A DAINA YIWA YAN FIM KUDIN GWORO
Daya daga cikin manya kuma uba a wasan hausa dan aslin garin kano a unguwar dala kuma malamin makarantar boko, wanda yafi fitowa a matsayin malami wato malam Kabiru na kwango, yaba cewa maabota kallan wasan hausa cewa dasu dai na yiwa yan wasan hausa kudin gworo, damin kuwanne mutun daka gani akwai irin sabon Allan dayakeyi kuma dukkan nin mu masu laifine sai wanda Allah ya ceta, kuma kusanncenka da Allah shine bauta masa da kuma bin kaidodin addinin musulunci.
Daya jiyo ga yan wasanhausa kuwa cewa yayi yakamata yan wasan hausan dasu kare mutuncin kansu a duk inda suke, kuma su daina shiga ta tsaraaice wacci har mutane zasu ringa yi masu kallan basu da tarbiyya, duk da cewa kuwanne tsuntsu kukan gidansu yakeyi, daga bisani kuma ya kamata masu shirya finafinai su ringa kula da addini da alada irinta malan bahaushe
An haifi malan kabiru na kwango dai a biyu ga watan februaty 1962 a unguwar Kan karofi a jihar kano Nageriya, ya kuma halacci tsangayoyin ilimi da dama, a inda ya sami shedar kamala karatun N.C.E. a marantar hurar da malami ta jihar kano, sannan kuma dan kasuwane, shine mutumin daya karbi takardun yabo da girmamawa a mtsayinsa na wanda yafi iya fitowa a matsayin uba a wasan hausa kamarsu
kadan daga cikin award din Nakwongo ya karba
Kano State Govt Awards
Best actor Father Role
2004
Kaduna State Govt Awards
Best Director Stage Drama
2002
Kaduna State Govt Awards
Best Actor Father Role
2004
Arewa Awards
Best Actor Father Role
2005
Yahoo Awards
Best Actor Father Role
2005
MOPPAN Awards
Best Actor Father Role
2004
MOPPAN Awards
Best Hausa Dialogue Promoter
2005



Domin samun hira da mujallar sautin hausa tayi da wannan jarumin na bidiyo saika nememo akan wannan e-mail din, nauku1991@yahoo.com, sautinhausa@gmail.com ku ka kira wannan lambar 07093015969, 07063427655





















A KWAI MASU YIN MURYAR IBRO DA YAWA

Daga Nauku Babir Bello siqo
waka dai baiwa ce wacce baa sayanta a kasuwa komai dunbin dukiyarka, saidai kaga masu basirsar suna ta bazakolin fasaharsu, domin idan wani yayi ya sami kudi wani kuma idan yayi sai an kwaceshi a hannun jama a domin dukan tsiya zai sha, amma idan kuma wani yayi sai kaga mutane suna tikar rawa kamar kafa zata karye kuma anata lika kudi a bin gwannin ban shaawa.
Wasu daga cikin fasihan mawakanma bayan muryarsu sai kaga harma tawani sukeyi, domin dazarar kayi kuskuren yin Magana agabansu to zasu iyayin muryarka kuma kaji kamar kaine kayi muryar, kuma su rera waka da muryar taka, irin wadannan fasihan mawaka anfi samunsu a cikin mawakan finafinan wasan hausa, kamar su Sadi Sidi sharifai mai muryar Ibro, sani larab mai muryar Yakubu Muhammed da dai sauransu.
Wakilinmu ya zanta da daya daga cikin wadannan fasihan mawakan wanda yayi wakar fim din Ibro dan Malam, da Daushe mai zamani, wanda da zarar ka kuskura kayi Magana a kusa dashi to tsab zaiyi waka da irin muryarka, wanda dan a salin garin Katsina ne a Unguwar Abbatuwa mai suna Kabir Bello Ciko, a cewarsa waka dai baiwace kuma ba a sayanta a kasuwa, kuma yasha gwagwarmaya a harkar fim da kuma kidan fiyano, domin har balaguron nemam Karin basira inda yaje har Zamfara yayi aiki a wani studio mai suna City sound Zamfara, sannan yace yayi gwagwarnmaya sosai a wannan harkar, amma yanzu yaga ranar hakuri domin nan bada dadewaba zai fara aiki a sabon studionsa daya bude a nan birnin Katsinan Dokko mai suna Siqo Musical Studio, amma kafin wannan lokacin yayi ayyuka a Studio dadama a matsayin makadi kamarsu, Extacy, Maitambura, M R B, City sound, da Boda studio, dana tambayeshi shin zai iya kirgamin yawan wakokinsa sai yace a gaskiya yanzu bazai iya kirga yawan wakokinsaba saboda su nada yawa.
Da kuma na tambaye shi shin yana fitowa a finafinai sai yakada baki yace yana fitowa domin ya fito a wasu finafinai kamarsu, Kacha, Kara, Rana inta fito,Sansanin Maharba,Ibro dan Malan, Daushe da kudi, Daushe mai zamani, Sabati, Sarkin aska, Natafi, Firgita samari, Daushe dan banga, Ibro mai duniya, Boda Album 3, da kuma da dama wadanda ke kan hanya
daga karshe dana tambaye shi ya akayi yana katsina kuma yasami dammar fitowa a wadannan finafinai sai yace ai basai lallai mutun yaze kano zaiyi fim ba, domin agarinsuma zai iyayin kumai, musamman nan mu katsina muna da frodusoshi, da directoci da dama sannan muna da lukashin kuma gwannatinmu ba harkar fim ne agaban taba, kaga kuwa muna da damar yin finafinai, saboda haka yammata da samari da suke fitowa su baro iyayensu suje kano dan harkar fim yakamata su tsaya agarinsu domin cigan garinsu suma, sannan mawakin yaba sauran mawaka shawara dasu kula wajan sarrafa harshensu domin duniyace ke sauraransu, sannan kuma yayi kira ga masoyansu dasu ringa yi musu addu a kuma da zarar sunji kuskure su gaggauta sanar dasu koda awayane domin wannan itace soyayyar gaskiya ba ayita zagin subasuba
idan kana bukatar wakar aure, ko ta siyasa. ko ta fim, ko kidan hausa ko naturanci, da ko wacce irin murya kakeso, zaka iya nemana akan wadanan lambobi kamar haka, +2347027077031,+2348050555096
ko kuma Addireshina kamar haka, W.T.C. Road Katsina














WASAN BARKUNCI
Wasan barkunci wato wasan camama wasane wanda nishadantarawa da fadakarwa, shin wasan camama na wannan zamanin fadakarwa yakeyi ko nishadantarwa saika rubuta ra ayin ka akan addreshin mu

Friday, June 12, 2009

WASU DAGA WAKOKIN TASKAR GANUWA
-Shugaba Na Mursalai
-Sayyadil Sadati
-Marhaba Muke da Zuwan Nabiyyi(S.A.W.)
-Ayarin Bege
-Gaishe Dakai Nurun
-Kai Nikeso ya Daha
-Ranar Mauludin Shugaba
-Hadin Kai
-Mui Bega ga Sayyadi
-Auren Nura da Zainab
-Auren Jamilu da Aisha
-Auren Hadiza da Zainab
-Auren Haruna da Zainab
-Auren Murjanatu
-Auren Shamsu
-Sani Mai Taya Elder
-AInusa Mai Taya Elder
-Bala Saulawa
-Abdu Yandoma
-Lawal Kaita
-Kabille Uban Zainab
-Milo Mai Rini (Sarkin Marina)
-Sokoto Dyeing
-Engr. Bala Banye
-Wakokin A.C.D.
-Gwamna Wamako
-Hajiya Maryam Mukhtar Shagari
-Ta-aziyyar Binta Saulawa
-S.I.Fatimiyya Production
-Azuba Q&C.C. Katsina
-Ni Ganuwa
-Hanyoyi Na Sadarwa




ADIRESHINA
Sabuwar unguwa, layi na uku, bayan sabuwar tasha jahar katsina nageriya
Lambar waya
+2340834487538, +2340724073003,+2340727870284
E-mail
ganuwa.gq.nu@gmail.com








FATANA GA MASOYANA
Inayiwa masoyana fatan alheri, da kuma fatan Allah dada kauna da soyayyar juna, sannan kuma ashirye nake da in karbi bakuncin kowa, muddin ka nemeni ta hanyar adireshena ko kuma kaitsaye,
Nagode allah yabar zumunci
.




TALLA
Idan kana bukatar ayima waka ta siyasa, aure, film, talla, taaziyya,jinjina, sarauta, suna, da dai sauransu, zaka iya tuntubata kaitsaye ko kuma ta hanyar adireshina, kuma ashirye muke da muyima aiki cikin sauki da inganci

Thursday, June 11, 2009

TASKAR GANUWA
Sunana misbahu sale ganuwa, mawakin wakokin siyasa , kuma dan asalin jahgar katsina a nageriya, an haifeni ashekara ta 1985 a cikin garin katsina a unguwar kufar kaura abirnin katsina, sannan nagirma awannan birnin mai albarka.
Na hallacci tsngayoyin ilimi da dama da taimakon iyayena, kuma na karbitakardun shedar kammalawa duk wata tsangaya dana halatta, da farko na halacci sir usman nagogo collage of Arabic and Islamic studies katsina state a inda na sami nasarar kamala karatun (nursery) sannan na halacci sabuwar unguwa primary school daga shekarar 1992 zuwa 1993, daga nan na hallacci government day secondary school daga 1998 zuwa 2002, haka zalika naje makarantar hurar da malamai dake collage sir usman nagogo katsina daga shekarar 2002 zuwa 2008, itama karbi tatardun kammalawa. Duk wadan nan gwagwarmaya danayi a fagen ilimi shiyabani dammar yin ayyukana cikin nutsuwa.
Bayan haka na fara waka a sheka ta 2000 a inda nafara jarraba fasahata da wakokin yaban manzan Allah (S .A. W.) kuma wakar gana farayi itace tantin masoya bege, daga nan sai kwakwalwa ta bude, a yanzu ina alfahari da wakoikina danayi domin duk inasansu